ABNA24 : Tuni dai sojojin Biritaniyar 100 suka isa a kasar ta Mali, domin taimaka wa shirin MDD na wanzar da zaman lafiya a kasar ta Mali, dake fama da matsalolin tsaro masu nasaba da gungun kungiyoyi masu ikirari da sunan jihadi.
Nan da mako guda ne kuma ake san sauren sojojin na Biritaniya zasu isa a kasar ta Mali, kamar yadda ma’aikatar tsaron Biritaniyar ta sanar.
Sojojinna Biritaniya zasu hade ne sauren dakarun kasa da kasa su 14,000 dake aikin tabbatar da zaman lafiya a kasar Malin dama yankin sahel dake fama da barazanar ayyukan ta’addanci.
Saidai jama’ar yankin da dama kamar na kasar Malin na adawa da ci gaba da kasancewar sojojin kasashen ketare musamman na kasashen yamma a kasashensu.
342/